Kotu ta tabbatar da shugabancin Mark na ADC, ta kori karar Abejide

ADC Aregbesola and Mark 750x430

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis ta tabbatar da shugabancin Sanata David Mark na jam’iyyar ADC.

A cikin hukunci da ya yanke, Mai Shari’a Musa Liman ya kuma kori karar da Dan Majalisa Leke Abejide ya shigar yana kalubalantar Mark da Ogbeni Rauf Aregbesola a matsayin shugaban da sakataren jam’iyyar na kasa saboda rashin hujja.

Mai Shari’a Liman ya amince da korafe-korafen farko da ADC, Chief Ralph Nwosu, Mark da Aregbesola suka shigar wadanda suka kalubalanci karar Abejide.

Mai shari’ar ya ce kotun ba ta da hurumi ta shiga harkokin cikin gida na jam’iyyar ADC, saboda haka ba za a iya yin hukunci a kai ba.

Ya kuma ce Abejide ba shi da damar shigar da karar ta fuskar doka, saboda bai nuna wa kotu cewa an tauye masa hakkinsa ba ta kowace hanya saboda kasancewar Mark a matsayin shugabancin.

Ya kuma ce Abejide, wanda memba ne na Majalisar Wakilai, bai bi hanyar cikin gida ta jam’iyyar ba don warware sabanin.

Mai Shari’a Liman ya kuma yanke hukunci kan batutuwa uku na babbar karar a madadin wadanda ake kara.

Kan ko Mark, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, da Aregbesola, tsohon Gwamnan Osun, sun zama shugabanin jam’iyyar bisa dokokin da suka dace, mai shari’ar ya yanke hukunci a kan Abejide, mai karar.

Ya ce mika shugabancin jam’iyyar da Nwosu ya yi wa Mark bai saba wa tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar ba.

Mai shari’ar ya yarda cewa taron jam’iyyar da ake jayayya a kai na ranar 2 ga Yulin 2025, taro ne na masu ruwa da tsaki wanda Majalisar Zartarwa ta Kasa (NEC0 ta jam’iyyar ta aka gudanar a ranar 29 ga Yuli, 2025, wanda ya fsamar da Mark da Aregbesola a matsayin shugabanin jam’iyyar kuma Hukumar Zabe ta Kasa 9INEC) ta sanya ido.

Saboda haka, Mai Shari’a Liman ya bayyana cewa zaman Mark da Aregbesola a matsayin shugabanin ADC na kan ka’ida kuma bisa ga kundin tsarin mulki, Dokar Zabe ta 2026 da dokar jam’iyyar.

Mai shari’ar ya kuma yanke hukuncin tara ta Naira miliyan 2 ga kowane mutum da ake kara, wanda Abejide ne zai biya.

Ya kuma yanke hukuncin tarar Naira miliyan 10 a kan lauyan Abejide dogaro da Dokar Zabe ta 2026.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here