Rikicin Kabilanci: An kone mutum 15 kurmus, an kashe wasu uku a Neja

Niger State map

An kashe kusan mutum 18 a wani rikicin kabilanci da ke da alaka da sabani kan filaye a karamar hukumar Rafi ta Jihar Neja, inda aka rawaito an kone mutane 15 har kurmus bayan da wasu mahara suka kona gida mai dakuna biyu da wuta.

Hari na baya-bayan nan ya faru a daren Talata a Angwan-Baago kusa da kauyen Godoro, inda aka tsare wadanda abin ya shafa a cikin gidan aka, sannan aka kone su da wuta, a cewar Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja.

‘Yan sanda sun ce an kuma kashe wani mutum a wani wuri daban, wanda hakan ya kai jimillar mutanen da suka mutu a rikicin zuwa 18.

Ana zargin rikicin ya samo asali daga wani sabani da ya dade kan fili tsakanin al’ummomi biyu a yankin.

Da farko, ‘yan sanda sun ce rikicin ya fara ne a ranar 29 ga Yuni, lokacin da wasu da ke dauke da makami da ake zargi suka harbi wani matashi mai shekaru 25, Ibrahim Musa a kauyen Godoro.

A cewar rundunar, kisan ya sa an kai wani harin ramuwar gayya, inda wata kungiyar ‘yan banga, da aka fi sani da Yansakai, ta rufe hanya tare da kashe Bashir Mazi mai shekaru 28.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, Wasiu Abiodun ya ce hare-haren na da nasaba da rikicin filaye da ya dade.

“A ranar 30 ga Yuni 2026 , da misalin karfe 2 na rana, an samu rahoton daga yankin Katako na Karamar Hukumar Rafi cewa a ranar 29 Yuni da misalin karfe 11:30 na dare a, ana zargi wasu mahara sun harbi Ibrahim Musa mai shekara 25 a kauyen Godoro, wanda ya mutu a nan ta ke.

“Sakamakon hakan, wata kungiyar Yansakai ta rufe hanya ta kashe Bashir Mazi mai shekara 28. Ana zargin wannan hari na da alaka da rikicin fili da yaki ci yaki cinyewa tsakanin kabilu biyu a yankin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here