Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta bai wa gwamnatin tarayya makonni hudu don warware rikicin ilimin gaba da sakandare

NLC

Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin makonni hudu domin kammala duk tattaunawar da ake yi a sashen ilimin gaba da sakandare a ƙasar nan.

Shugaban kungiyar, Joe Ajaero, ne ya sanar da hakan a taron manema labarai na gaggawa da aka gudanar a Abuja bayan wani dogon taro da kungiyar ta yi tare da shugabannin ƙungiyoyin ma’aikata na jami’o’i, kwalejoji, da makarantu na gaba da sakandare.

Kungiyar ta ce wannan mataki ya biyo bayan shekaru da dama na yarjejeniyoyi da gwamnati ta gaza cikawa da kuma ƙarancin kuɗin da ake ware wa harkar ilimi, wanda hakan ke jawo yawaitar yajin aiki da rashin kwanciyar hankali a jami’o’i, kwalejojin kimiyya da fasaha, da kuma kwalejojin ilimi.

Haka kuma, kungiyar ta jaddada cewa ba za ta ci gaba da zuba ido ba yayin da gwamnati ke nuna halin ko in kula ga matsalolin da ke addabar bangaren ilimi.

A cewar NLC, wannan wa’adi da ta bayar ya zama dole domin tabbatar da cewa gwamnati ta dauki matakai masu inganci wajen magance matsalolin da suka daɗe suna janyo tsaiko a harkokin karatu.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa idan gwamnati ta kasa cika wannan wa’adi, za ta ɗauki matakan da suka dace don kare muradun ma’aikata da cigaban ilimi a ƙasar nan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here