Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga matasa biyu da suka kashe malamin jami’a a Kano

Hanging 0 750x430

Wata babbar kotu a Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu matasa biyu Aliyu Hussaini da Amir Zakariyya bisa samun su da laifin kashe malamin jami’a Buhari Imam, wanda yake a jami’ar Northwest da ke Kano, ta hanyar caka masa wuƙa.

Hussaini, mazaunin Sheka Sabuwar Abuja Quarters, da Zakariyya, mazaunin Unguwar Malam a ƙaramar hukumar Kumbotso, an same su da laifuka guda uku na haɗa baki, fashi da makami, da kuma kisan kai.

Mai shari’a Fatima Adamu ta tabbatar da cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da shari’arsu fiye da shakku, sannan ta ce aikinsu ya nuna rashin tausayin ɗan Adam gaba ɗaya.

Kotun ta yanke musu hukuncin shekaru biyar a gidan yari bisa laifin haɗa baki, shekaru goma bisa fashi da makami ba tare da zaɓin tara ba, sannan ta yanke musu hukuncin kisa ta rataya bisa kisan kai.

Bincike ya nuna cewa laifin ya faru ne a ranar 11 ga watan Yuni da misalin ƙarfe 3:30 na asuba a Sheka Sabuwar Abuja Quarters, inda mutanen biyu suka haɗa baki, suka ɗauki makamai irin su wuƙa da adda, suka yi wa malamin fashi suka kuma caka masa wuƙa a ciki, cinyoyi da baya har ya mutu.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa masu gabatar da ƙara sun kawo shaidu uku tare da gabatar da rahoton likita da hotunan mamacin a matsayin hujjoji.

Masu laifin sun musanta aikata laifin, yayin da lauyansu Haruna Saleh-Zakariyya ya roƙi kotu ta yi musu sassauci.

Kotu ta ce Laifukan sun saɓa wa tanadin sashe na 97(1), 298(c), da 221(a) na dokar hukunta laifuka ta jihar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here