Gwamnatin jihar Neja ta bada umarnin kama mutanen da ke tara gashin Dada

Umar Bago 750x430

Gwamnan jihar Neja, Umar Bago, ya umarci jami’an tsaro da su damke masu tara gashin Dada a kan su musamman a Minna, babban birnin jihar.

Da yake jawabi a wajen taron tsaro na masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidan gwamnati a ranar Talata, Bago ya ce ya kamata jami’an tsaro su yanke gashin irin wadannan mutanen da aka kama tare da sanya musu tara.

Taron ya samu halartar hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya.

Gwamnan na Neja ya ce gwamnatinsa ba ta da hurumin nuna wariyar launin fata.

“Duk wanda kuka same shi da tarin sumar Dada a kan sa ku kama shi”.

“Babu wanda ya isa ya yi kowane irin aski a cikin Minna, na ba jami’an tsaro umarnin daukan mataki.”

Karanta: NiMet ta yi hasashen samun zazzafar rana da tsawa na kwanaki 3

Bago ya kuma umurci jami’an tsaro da su kama duk wani mai dauke da makamai a jihar a matsayin ɗan fashi da makami.

Gwamnan ya kuma sanya dokar takaita zirga-zirgar babura masu kafs uku daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe a Minna.

Bago ya ce, an kebe babura wadanda za su yi amfani wajen gaggawar kai mara lafiya asibiti, inda ya kara da cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba ya kalli yadda masu aikata laifuka ke ci gaba da aikata miyagun ayyuka a jihar.

Bago ya nemi hakiman gundumomi, kauye, da masu unguwanni da su tabbatar da cikakkun takardu na mazauna yankunansu.

Ya kara da cewa, duk wani gini da aka samu yana dauke da masu aikata laifuka ko kuma ana sayar da muggan kwayoyi za a lalata shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here