NiMet ta yi hasashen samun zazzafar rana da tsawa na kwanaki 3

Sunshine

Hukumar kula da yanayi ta ƙasa (NiMet) ta yi hasashen fuskantar zazzafar rana da tsawa daga ranar Laraba zuwa Juma’a a fadin Najeriya.

Rahoton yanayin na NiMet da aka fitar a ranar Talata a Abuja, ya yi hasashen sararin samaniyar ranar Laraba tare da yiwuwar tsawa a wasu sassan jihohin Adamawa da Taraba da yammacin ranar.

Ya bayyana cewa ana sa ran ganin sararin samaniyar rana mai karancin giza-gizai a yankin Arewa ta Tsakiya inda ake sa ran za a yi tsawa a sassan jihohin Kwara da Neja.

“A washegari, ana sa ran za a yi tsawa a sassan jihohin Kogi, Kwara da Filato.

“A yankin kudu, ana sa ran samun giza-gizai tare da yiwuwar yin tsawa a safiyar Laraba a sassan Oyo, Ogun, Ondo, Osun, Delta, Lagos, Rivers, Cross River da Akwa Ibom.

Karin karatu: Gwamnatin Kano ta biya Naira Biliyan 21 daga cikin Naira Biliyan 48.6 na kudaden fansho da gwamnatocin Kwankwaso da Ganduje suka gadar mata

“Da rana da maraice ana sa ran tsawa a sassan jihohin Imo, Abia, Ebonyi, Bayelsa, Rivers, Cross River da Akwa Ibom,” in ji hasashen.

NiMet ta yi hasashen zazzafar rana a yankin arewacin kasar nan a ranar Alhamis da yiwuwar yin tsawa da rana ko maraice a wasu sassan jihar Taraba.

Hasashen ya ce sararin samaniyar da ke da karancin gizagizai a fadin yankin Arewa ta Tsakiya a lokacin safiya.

A cikin wannan rana, ana sa ran zazzafar tsawa a wasu sassan babban birnin tarayya, Benue, Plateau da Nasarawa.

Ya kara da cewa, “A yankin kudancin kasar nan, ana sa ran samun gajimare da za a yi tsawa da safiya a sassan jihohin Bayelsa, Ribas, Cross River, Akwa Ibom da Legas da rana da kuma yamma.”

Hukumar ta kuma yi hasashen zazzafar tsawa a wasu sassan Imo, Anambra, Abia, Ondo, Osun, Oyo, Bayelsa, Rivers, Cross River, Delta da Edo a ranar Alhamis.

NiMet ya yi hasashen zazzafar rana a ranar Juma’a a kan yankin arewacin kasar inda ake hasashen za a yi tsawa a sassan kudancin jihar Adamawa da Taraba da kuma Kaduna da rana ko yamma.

“Ana sa ran sararin samaniyar da ke da karancin gizagizai a kan yankin Arewa ta Tsakiya tare da yiwuwar yin tsawa a safiya a sassan babban birnin tarayya da jihohin Neja.

Karanta: Zargin cin hancin miliyan 5.2: NSCDC ta bada umarnin a tsare wasu jami’anta 

“A washegari, ana hasashen za a yi tsawa a wasu sassan jihohin Kwara, Kogi, da Neja.

“A yankin kudu, ana sa ran samun gajimare a cikin safiya tare da yiwuwar tsawa a sassan Oyo, Ogun, Legas, Bayelsa da Delta,”.

Hukumar ta kuma yi hasashen zazzafar tsawa a sassan jihohin Abia, Imo, Ogun, Oyo, Ondo, Cross River, Akwa Ibom, Delta, Rivers da Bayelsa.

“Ana iya fuskantar Zazzabi a yawancin sassan ƙasar, wanda ka iya jefa mutane cikin haɗari saboda zafin rans, don haka ya kamata mutane su kasance a wurare masu kyau da kuma sanyi.

“A sha ruwa mai yawa, a yi allurar rigakafin cutar sankarau, a kula da tsafta ta hanyar wanke hannu akai-akai da kuma guje wa cunkoso a kananan wurare.

“Yi amfani da abin rufe fuska don rage yiwuwar kamuwa da cuta da kuma guje wa kusanci da waɗanda abin ya shafa.

“A kauce wa shiga rana a sa’o’i na rana (12pm zuwa 3pm) kuma s kare kanku daga hasken rana kai tsaye,” in ji ta.

Hukumar ta shawarci jama’a da su yi taka tsantsan domin iska mai karfi na iya tunkarar ruwan sama a wuraren da ake iya samun tsawa.

“An shawarci ma’aikatan jirgi da su samu takamaiman rahoton yanayi na filin jirgin sama.

“An shawarci mazauna garin da su ci gaba da sanar da hukumar ta NiMet ko ziyarci shafin internet (www.nimet.gov.ng),” in ji shi. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here