KHAIRUN da Ma’aikatar Lafiya ta Kano sun sanya hannu kan MoU domin karfafa ilimin kiwon lafiya da horo

725191745 1002014105870009 4825316996888196957 n 750x430

Jami’ar Khalifa Isyaku Rabiu da ke Kano (KHAIRUN), ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (Memorandum of Understanding) da Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano domin karfafa hadin gwiwa a fannin ilimin kiwon lafiya, horar da kwararru, bincike da gudanar da ayyuka.

An kammala yarjejeniyar ne a wani bikin sanya hannu da aka gudanar a ranar Alhamis a hedikwatar Ma’aikatar da ke Kano.

Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdulrashid Garba, wanda ya jagoranci tawagar KHAIRUN, ya bayyana hadin gwiwar a matsayin babbar nasara wajen nuna kudirin Jami’ar na samar da ci gaban bangaren lafiya.

Farfesa Garba ya isar da godiya da fatan alheri daga Gidauniyar Muhammad Rabiu, Kwamitin Gudanarwa na Jami’ar, Majalisar Gudanarwa, Majalisar Zartarwar Jami’a ga Kwamishinan Lafiya, Dr. Abubakar Labaran Yusuf da Ma’aikatar saboda goyon baya da hadin gwiwa da suke ci gaba da bayarwa.

Ya ce yarjejeniyar tana nuna hangen nesan bangarorin biyu na habaka ilimin kiwon lafiya da inganta bayar da ayyuka a Jihar Kano.

Shugaban Jami’ar ya kuma gode wa Kwamishinan da manyan jami’an Ma’aikatar saboda kudirinsu da hadin gwiwa da ya ce sun tabbatar da kammala yarjejeniyar cikin nasara.

Ya kara yaba wa gudummawar Dean na Shashen Lafiya, Farfesa Muhammad Yalwa Gwarzo, da Rijistaran Jami’ar, Malam Yusuf Datti, yana mai cewa juriya da sadaukarwarsu sun kasance masu tasiri wajen cimma nasar yarjejeniyar.

Da yake jawabi a wurin taron, Kwamishinan Lafiya, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya yi maraba da tawagar KHAIRUN kuma ya yaba wa Jami’ar bisa amincewa da kokarin Ma’aikatar da Gwamnatin Jihar Kano wajen tallafawa ilimi da ci gaban lafiya.

Ya sake jaddada kudirin Ma’aikatar na tallafawa Jami’ar kuma ya jaddada rawar da jami’o’in masu zaman kansu ke takawa wajen taimaka wa gwamnati wajen karfafa fannin ilimi da lafiya.

A cewarsa, ana sa ran hadin gwiwar zata ba da gudummawa mai ma’ana ga ayyukan kiwon lafiya da inganta walwalar jama’a.

Dr. Yusuf ya kara tabbatar wa Jami’ar cewa za a ba su damar amfani da asibitocin gwamnatin jihar a ko’ina a cikin Kano domin horar da daliban KHAIRUN a aikace da ba su kwarewar aiki.

SolaceBase ta ruwaito cewa taron ya kare da sanya hannu bisa ka’ida kan Yarjejeniyar Fahimta Juna (MoU) tsakanin Shugaban Jami’ar da Kwamishinan, wanda ke alamta farkon hadin gwiwar da nufin habaka nagarta a ilimin kiwon lafiya, bincike da cigaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here