Kano Leads ta yi kira ga gwamnatin Kano ta samar da wadatattun gurin zubar da shara a jihar

Kano Leads, ma'aikatar, muhalli, sauyin, yanayi, jihar, kano
Kungiyar tabbatar da ci gaban jihar Kano KANO LEADS, tayi kira ga gwamnatin jihar da ta kara kaimi wajen samar da wajan zubar da shara a jihar, ta yadda ake...

Kungiyar tabbatar da ci gaban jihar Kano KANO LEADS, tayi kira ga gwamnatin jihar da ta kara kaimi wajen samar da wajan zubar da shara a jihar, ta yadda ake zubar da shara barkati a fadin jihar.

Kiran ya fito ne ta bakin sakataren kungiyar, Abubakar Sa’id yayin wata ziyara da ya kai ma’aikatar muhalli ta jihar kano ranar Laraba.

Sakataren kungiyar ya koka kan yadda ake samun cunkoso da kuma yawan zubar da shara barkatai a jihar Kano.

Karin labari: Gwamnatin Kano ta karyata barkewar cutar kyanda

“Wannan kungiya tana kira ga gwamnatin jihar kano da ta duba halin da wasu unguwannin jihar Kano ke ciki musamman yadda ake zubar da shara ba bisa ka’ida ba, wanda rashin kauwamaman gurin zubar da sharan ne ke haifar da haka” inji Abubakar.

“Yanzu yana yi ne na zafi, a duba halin da al’umma ke ciki musamman a lokacin dumamar yana yi, ya kamata a samar da abubuwan da za su rage cunkoso a wasu unguwanni da kasuwan nin jihar da zai taimaki al’umma baki daya.”

Karin labari: Sudan ta amince shigar da agaji ta ƙasashe maƙwabta

A nasa jawabin kwamishinan ma’aikatar muhalli ta jihar Kano, Alhaji Nasiru Sule Garo, ya yaba da ziyarar da kungiyar ta kai masa.

“Tabbas na yaba da tunanin wannan kungiya ta Kano Leads, domin ba kowacce kungiya ce ke kokarin yin nazarin da zai taimaki al’umma ba.

“Kunyi tunani mai kyau matuka kuma kamar yadda ku ka zo da wannan kuduri haka wannan ma’aikata karkashin gwamnatin Kano ke shiga lungu da sako wajen ganin an samar da wadataccen waje da zai rage cunkoso da samar da wajen zuba shara” in ji Nasiru.

Karin labari: An shiga ruɗani bayan kisan limami a Zamfara

Ya kara da cewa “wannan yanayi da aka shigo na zafi akwai matakai da dama da wannan ma’aikata ke bi kuma ta dauka a lokacin dumamar yana yi da za ta samarwa al’umma mafita.”

Garo ya yi alkawari da cewa kofa a bude ta ke ga duk wani abu da ya shigewa kungiyar duhu da ta kokarta kawo korafin da zai taimaki al’umma karkashin ma’aikatarsa da ya jibanci muhalli da sauyin yanayi don magance matsalar cikin gaggawa, ko ta tuntubi gwamnati kai tsaye.

Karin labari: Majalisar dokokin Edo ta fara shirin tsige Shaibu

Taron ya maida hankali ne kan samarwa unguwannin da ke fadin jihar Kano mafita kan yanayi na cunkoso da zubar da shara a wasu wuraren da ba bisa ka’ida ba, musamman a lokacin zafi da kan iya haifar da illa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here