Majalisar dokokin Edo ta fara shirin tsige Shaibu

Philip Shu'aibu, edo, tsige, majalisar dokoki
Majalisar dokokin jihar Edo da ke kudancin Najeriya sun fara wani yunƙuri na tsige mataimakin gwamnan jihar Philip Shaibu. An sanar da hakan ne a zauren...

Majalisar dokokin jihar Edo da ke kudancin Najeriya sun fara wani yunƙuri na tsige mataimakin gwamnan jihar Philip Shaibu.

An sanar da hakan ne a zauren majalisar a ranar Laraba, inda bayanai ke nuna cewa yunƙurin ya samu goyon bayan ‘ƴan majalisa 21 a cikin 24 da ke majalisar.

A ranar Talata ne aka gabatar da wani ƙorafi kan mataimakin gwamnan, inda ake zarginsa da rantsuwa kan ƙarya da kuma bayyana wasu batutuwa na sirri na gwamnatin jihar.

Karin labari: Rikicin Sudan zai iya janyo yunwa mafi tsanani a duniya – WFP

Kafar yada labarai ta Channels ta bayyana shugaban masu rinjaye a majalisar na cewa yawan waɗanda suka goyi bayan tsige mataimakin gwamnan sun kai kashi biyu bisa uku da ake buƙata, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Inda kakakin majalisar, Blessing Agbebaku ya bai wa magatakardar majalisar ya miƙa takardar tsige Shaibu.

Dangantaka tsakanin gwamnan jihar, Godwin Obaseki da mataimakin nasa na ƙara tsami a baya-bayan nan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here