CBN ya gargadi Jama’a da su yi taka tsan-tsan da jabun kudaden da ke zagayawa

Old and New Naira Notes 750x430
Old and New Naira Notes 750x430

Babban bankin kasa CBN ya gargadi ‘yan Najeriya da su yi taka-tsan-tsan da jabun kudaden da ke zagayawa.

Babban bankin ya yi wannan gargadin ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Ya shawarci bankunan ajiyar kudi da Ma’aikatun kudi da kasuwannin chanji, da jama’a kan su lura tare da aiwatar da matakan da suka dace.

Karanta Wannan: Hukumar kula da gidajen Yari ta musanta zargin fitar da Emefiele daga gidan Gyaran hali  

Babban bankin na CBN ya tabbatar wa jama’a cewa yana aiki tare da jami’an tsaro domin kamo wadanda ke da alhakin yada kudaden jabun.

Har ila yau, ya karfafa wa jama’a gwiwa da su rungumi wasu hanyoyin biyan kudi don hada-hadar yau da kullum da nufin rage yada takardun kudi na jabu.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here