Gwamna Yusuf ya nada manyan sakatarori 21, tare da sake sauyawa wasu 8 wuraren aiki

FB IMG 1699444381726 750x430
FB IMG 1699444381726 750x430

Gwamnan jihar Kano Abba Yusuf ya amince da nadin manyan sakatarori 21 na ma’aikatan jihar.

Hakazalika, gwamnan ya sauyawa wasu takwas wuraren aiki a wani sabon yunkuri na karfafa ma’aikatun gwamnati.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai na Gwamnan Sunusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar a Kano.

Sanarwar ta ce an yi hakan ne “domin sake farfado da ma’aikatun jihar don samar da ayyukan yi”.

Karanta Wannan: CBN ya gargadi Jama’a da su yi taka tsan-tsan da jabun kudaden da ke zagayawa

Yace amincewar gwamnan na kunshe ne a wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan gwamnati, Alhaji Abdullahi Musa.

A cewar sanarwar, wadanda aka nada sune Aminu Shuaibu Rabo da Abdul Saad Zakirai da Usman Bashir Maikano da Aminu Yusuf Kura.

Sauran su ne Umar Mahmud Jalo da  ​​Kubra Ahmad Bichi da Dan’asabe Yahaya da Ibrahim Boyi da kuma Abubakar Sadiq Mahmud.

wadanda aka sakewa wurin aiki su ne Kabiru Saidu Magami da Musa Tanko, da Aliyu Yakubu Garo.

Sauran sun hada da Sani Bashir Yola da Hafsat Iliyasu Aliyu da Aisha Abba Kailani, da Salahu Isah Habib da Salisu Mustapha.

Gwamnan ya umurci sabbin manyan sakatarorin da aka nada da su gudanar da ayyukansu cikin himma da kwarewa wajen inganta manyan manufofin gwamnatinsa.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here