Gwamna Radda zai bincike wadanda suka ci gajiyar shirin Anchor Borrowers  

Gov Radda
Gov Radda

Gwamnan Jihar Katsina Umar Dikko Radda, ya kaddamar da wani kwamiti mai mutum 12 da zai binciki wadanda suka ci gajiyar shirin da gwamnatin tarayya ta aiwatar da shi wato Anchor Borrower Programme a jihar.

Babban bankin kasa ne, ya bullo da shirin don bunkasa tattalin arziki tsakanin kananan manoma da kamfanoni da ke da hannu wajen samarwa da amfanin gona.

CBN
Babban bankin Kasa CBN

Jigon shirin shi ne bayar da rance ga manoma masu karamin karfi don bunkasa noma, tare da rage kudaden shigo da abinci daga kasashen waje.

Sai dai rahotanni na nuni da cewa, manoman ko dai ba su mayar da rancen da aka ba su ba, ko kuma wadanda ke da alhakin karbo rance da rabawa sun hau kan kudin.

Karanta wannan:Ya kamata a kara wa’adin daina karbar tsoffin takardun kudi – yan Najeriya

Mai taimakawa gwamman kan harkokin yada labarai, Malam Ibrahim Kaula, shi ne ya bayyana hakan a Katsina a ranar Asabar, inda yace gwamnan ya umarci kwamitin da ya binciki yadda aka gudanar da shirin.

Kaula, ya kara da cewa, Radda ya bukaci kwamitin da ya tabbatar da mambobinsa sun yi aiki tukuru.

Ana sa ran kwamitin zai gabatar da rahotonsa nan da makonni biyu, daga ranar 7 ga watan Disambar da muke ciki.

 

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here