Wani lamari mai kama da Wasan kwaikwayo ya faru a Kano, yayin da hukumar tattara haraji ta tarayya FIRS ta rufe shalkwatar kamfanin rarraba wutar lantarki na KEDCO kan bashin kuɗaɗen haraji, shi ma kamfanin a wani martani na ramuwar gayya ya katse wutar lantarki a ofisoshin hukumar.
Da ya ke fayyace maƙasudin wannan taƙaddama wani ma’aikacin KEDCO wanda ya yi magana da SolaceBase bisa sharadin sakaya sunansa, a yau Alhamis, ya bayyana cewa babban ofishin kamfanin KEDCO na Kano ya kasance a kulle har tsawon kwanaki tara ba tare da an bai wa wani ma’aikaci izinin shiga ba.
Inda kan haka a wani mataki na ramuwar gayya, rahotanni suka ce, KEDCO ya katse wutar lantarkin ga dukkan ofisoshin hukumar ta FIRS da ke jihar Kano, lamarin da ya kara tada jijiyoyin wuya a tsakanin sassan biyu.
Har zuwa lokacin fitar da wannan rahoto, kokarin samun amsa a hukumance daga KEDCO da FIRS ya ci tura.
SolaceBase ta sha kiran jami’in hulda da jama’a na KEDCO, Malam Sani Bala, amma layin wayarsa bai shiga ba.
Wakilinmu ya kuma ziyarci ofishin FIRS da ke kan titin Gwarzo inda ya zanta da ofishin kula da basussuka, amma ma’aikatan sun ki bayar da cikakken bayani kan lamarin.
Sai dai wani mai bincike a FIRS ya bayyana cewa bashin harajin KEDCO ya samo asali ne tun shekaru 6 da suka gabata, wanda ya samo asali daga gwamnatocin baya.













































