Gwamnatin Kano ta haramta sake sarrafa sharar kayan asibitoci

Kano Map

Gwamnatin jihar Kano ta haramta wa masana’antu sake sarrafa shara saye ko sayar da kayan aikin asibitoci da sharar magunguna, inda ta yi gargadin cewa masu karya dokar za su fuskanci tsauraran hukunci.

A ranar Juma’ar nan ne mai bai wa gwamna shawara kan muhalli da tsaftar muhalli Injiniya Abdullahi Shehu Bichi, a yayin ziyarar duba kananan masana’antu na Dakata ya bayyana hakan.

SolaceBase ta ruwaito cewa ziyarar wani bangare ne na sanya ido kan yadda gwamnati ke yin aikin tsaftar mahalli na karshen wata a fadin cibiyoyin gwamnati da masana’antu da wuraren kasuwanci.

Injiniya Bichi, wanda ya bayyana damuwarsa kan rashin kyawun ayyukan tsaro a wasu masana’antu, ya jaddada cewa gwamnati na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaro da kuma sarrafa shara yadda ya dace.

Kwamitin duben tsaftar, ya kuma nemi haɗin kan shugabanni da masu masana’antu don yin aiki tare da jami’an gwamnati wajen yin nazari da inganta matakan tsaro don kare rayuka dukiya da kuma muhalli.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here