Matatar Mai ta Dangote ta ce ta daina sayar da fetur da Naira

IMG 20240829 WA0005

Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da cewa ta dakatar da sayar da man fetur da kuɗin Najeriya wato naira.

Kamfanin ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya aika wa dilallan man fetur kuma ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba.

Sanarwar ta ce ”Matatar man fetur ta Dangote ta dakatar da sayar da fetur a naira na wani lokaci. Hakan ya zama wajibi ne saboda kauce wa rashin daidaito da ake samu tsakanin ribarmu da kuɗin da muke sanya wa masu sayen ɗanyan mai wanda a yanzu galibi da dala muke yi.”

Karanta: Matatar man Dangote zata mayar da kudi ga yan kasuwar data sayarwa fetur da tsada

Kamfanin ya kuma ƙara da cewa bisa wannan dalilin, wajibi ne su sauya kuɗin da suke sayar da man domin ya yi daidai da kuɗin da suke sayen ɗanyen mai na wani ɗan lokaci.

Sanarwar ta kuma ce da zarar matatar ta karɓi jiragen dakon mai da aka saya da naira daga kamfanin NNPC, za ta ci gaba da sayar da man fetur ɗin da naira.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here