Fubara ya gaza hana tsageru lalata bututun mai- AGF

Siminalaye Fubara 750x430

Babban Lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ya yi zargin cewa gwamnan jihar Rivers da aka dakatar a yanzu Siminalayi Fubara, ya gaza magance duk wata barna da tsageru masu fasa bututun mai a jihar ke yi.

Fagbemi ya yi wannan zargin ne yayin da yake kare matakin da shugaban kasa Bola Tinubu ya dauka na kafa dokar ta-baci a sa’o’i kadan da suka gabata.

Ya ce duk da cewa gwamnan ba shi da laifi kai tsaye, amma ya kasa hana ‘yan bindiga fasa bututun mai.

Fagbemi ya bayar da hujjar cewa kasancewar al’ummar kasar sun kusan dogaro da danyen man fetur, duk wanda ya taba bututun mai ba makiyin Rivers ne kadai ba har ma da Najeriya.

Karanta: Yanzu-yanzu: Tinubu ya rantsar da sabon shugaban jihar Rivers, Ibas

Ministan ya ce dole ne a dakatar da Fubara da ‘yan majalisar dokokin jihar saboda sun kasa tabbatar da kyakkyawan yanayi na shugabanci a jihar.

A ranar Talata ne Tinubu ya kafa dokar ta-baci a jihar Ribas, inda ya dakatar da Fubara, mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da dukkan zababbun ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas na tsawon watanni shida.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here