Shugaban kasa Bola Tinubu ya rantsar sabon shugaban na jihar Rivers, Vice Admiral Ibok-Étè Ibas (mai ritaya).
Tinubu ya rantsar da Ibas ne da misalin karfe 03:00 na rana a fadar gwamnati da ke Abuja.
Takaitaccen bikin ya samu halartan shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi, SAN, da kuma babban sakataren shugaban kasa, Mista Hakeem Muri-Okunola.
karin labari: Majalisar Dattawa ta karbi wasikar Tinubu don yin muhawara kan dokar ta ɓaci a jihar Rivers
Ibas ya isa fadar shugaban kasa da misalin karfe 12:48 na rana.
A daren ranar Talata ne Tinubu ya kafa dokar ta-baci a jihar Rivers, inda ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa Ngozi Odu, da dukkan zababbun ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida sakamakon rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar.













































