‘Yan sanda sun kama Fasto Moses Enyiaka bayan da ya ɗirka wa wani ƙaramin yaro harsashi har lahira a Jihar Imo.
An kama Moses ne bisa zargin harbe yaron har lahira saboda ya harba abubuwa masu qara a cikin harabar coci.
Lamarin ya faru ne a lokacin da ake tsaka da ibadar tarbar Sabuwar Shekarar 2025 a Cocin St Columbus Parish da ke yankin Amamio na Ƙaramar Hukumar Ikeredu ta jihar.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo, ASP Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin, da cewa sun fara bincike domin gano ainihin musabbabin abin da ya faru.
Jami’in ya ce ba su san yadda limamin cocin ya samu bindigar da ya yi amfani da ita ba, amma suna ci gaba da bincike.