Gobara ta sanya Mutane 120 rasa gidajen su a Ilorin

Fire outbreak
Fire outbreak

Wata gobara da ta afku a rukunin gidaje na Megida Onikanhun da ke Edun Isale a karamar hukumar Ilorin ta Kudu, ta haddasawa mutane 120 rasa gidajen su, tare da kone dakuna 44 na wani gini da wani masallaci.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai na hukumar kashe gobara ta jihar Kwara Hassan Adekunle, ya fitar ranar Litinin a Ilorin.

Karanta wannan: Gwamnatin Kano za ta yi bincike akan gobarar Sakatariyar Gwale

Ya ce a ranar 15 ga watan Janairun 2024, da misalin karfe 11:08, hukumar kashe gobara ta jihar Kwara ta sami rahoton tashin gobara a harabar rukunin gidajen Megida Onikanhun dake Edun Isale, a karamar hukumar Ilorin ta Kudu.

Adekunle ya jajanta wa wakilin Magaji Megida Onikanhun, Kuranga Adebayo.

Ya yaba da kokarin hukumar kashe gobara amma ya ce lamarin ya sanya mutane sama da 120 sun rasa matsugunai, wanda ya shafi dakuna 44 da wani masallaci amma ba a sami asarar rai ba.

Karanta wannan: Gwamna Namadi ya jaddada aniyarsa ta bunkasa Ilimi da Lafiya a Jihar Jigawa

Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Falade Olumuyiwa, ya bukaci jama’a da su rika yin taka tsantsan da wuta, musamman a wannan lokaci.

Ya kuma bukaci jama’a da kada su yi kasa a gwiwa wajen kiran hukumar kashe gobara a kan lokaci a duk lokacin da aka samu gobara a yankunansu, domin hakan zai ceto rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here