Dakarun bataliya ta 192, sashe na 81, na rundunar sojojin kasar nan, sun kama wasu da ake zargin manyan dilolin masu safarar miyagun kwayoyi ne a kan iyakar Balogun da ke jihar Ogun.
Sanarwar da Daraktan yada labaran rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ya ce sojojin sun gano haramtattun abubuwa guda 296, wadanda ake kyautata Aaron miyagun kwayoyi ne, da aka boye a cikin wata mota kirar Sienna 2001 mai lamba Legas APP 129 EF.
Karanta wannan: Sojojin Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare ta kasa a Gaza
Wadanda ake zargin, Adigun Olatunji mai shekaru 54 da kuma Michael Atanda mai shekaru 18, dukkansu ‘yan garin Ilara Imeko a karamar hukumar Afun ta jihar Ogun amma kuma suna zaune a jamhuriyar Benin, an tsare su ne bayan wani yunkurin ba da cin hancin Naira miliyan 12 ga sojoji.
Binciken da sojoji suka gudanar ya nuna cewa an yi safarar haramtattun kayan ne daga jamhuriyar Benin ta cikin kauyukan Ilara dake kan iyaka da zuwa Ifo a jihar Ogun.Isra’il
Karanta wannan: Mai Magana da yawun gwamnan jihar Borno Isah Gusau ya rasu
Nwachukwu, yace masu fataucin kwayoyin, wadanda ke yin safarar daga wata kasa zuwa wata, sun shafe watanni biyar suna shirya yadda zasu shigo da tabar wiwi domin kai wa abokan huldarsu.
Wasu daga cikin kayayyakin da aka kwace sun hada da katin shaidar zama dan kasa na jamhuriyar Benin da katin shaidar dan kasa na Najeriya sai kananan wayoyin hannu guda biyu da lasisin tuki na jamhuriyar Benin da fasfo na kasa da kasa na jamhuriyar Benin da layin waya na jamhuriyar Benin guda shida, sai lasisin tuki na Najeriya da kuma kudin da ya kai Naira 52,700.
Ya kara da cewa za a mika wadanda ake zargin da kayayyakin da aka kama ga hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA domin gurfanar da su gaban kuliya.