Sojojin Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare ta kasa a Gaza

download
download

Rundunar sojojin Isra’ila na fadada hare-hare ta kasa a tsakiyar zirin Gaza, kusan wata uku da aka soma yakin.

Wani jami’in Majalisar dinkin Duniya ya bayyana matukar damuwa game da yadda aka kai hari kan sansanonin yan gudun hijra da ya cika makil da mutanen da suka rasa matsugunnai.

Karanta wannan: Barau Ya Mika Ta’aziyar Sa Ga Iyalain Tsohon Kakakin Majalisar wakilai, Ghali Na’Abba

Rundunar sojin ta Isra’ila ta ce ta kai hari kan wata hedikwatar Hamas ta karkashin kasa a Jabalia da ke arewacin Gaza tare da kai hare-hare ta sama a Khan Younis a kudanci.

Karanta wannan: Kudadenku ba gara ba zago a bankuna-Bankin CBN

Kakakin hukumar lafiya ta duniya ya shaida wa kafar yada labarai ta BBC cewa abokan aikinsa sun shiga tashin hankali a ko ina a Gaza.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here