Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, ya yabawa ‘yan majalisar bisa jajircewar da suka yi a zaman tsaro na kasafin kudin 2025.
Akpabio ya jaddada rawar da suke takawa wajen ganin an samar da ingantaccen tsarin kudi na wannan shekara.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jagorantar zaman majalisar dattawa bayan hutun makonni biyu da suka tafi kuma suka dawo a ranar Talata.
Karin karatu: Majalisar Wakilai ta roƙi NLC ta fasa yajin aiki kan ƙarin kuɗin waya
Bayan amincewar da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi na kudirin kafa kwamitocin raya kasa a yankuna daban-daban, majalisar dattawa ta yi gyare-gyare kadan, inda ta nada sabbin shugabanni da mataimakansu da za su rika kula da wadannan kwamitocin.
Akpabio ya ce, “Sanata Babangida Hussaini da Sanata Muntari Dandutse za su yi aiki a matsayin shugaba da mataimakin shugaban kwamitin majalisar dattawa kan hukumar raya yankin Arewa maso Yamma.
“Hakazalika, an nada Sanata Orji Uzor Kalu da Sanata Kenneth Eze a matsayin shugaba da mataimakin shugaban kwamitin majalisar dattawa a hukumar raya Kudu maso Gabas, yayin da Sanata Titus Zam da Sanata Isa Jibrin za su jagoranci kwamitin majalisar dattawa mai kula da hukumar raya yankin Arewa ta tsakiya. ”
Abdul Ningi ya koma daga kwamitin kula da yawan jama’a ya zama shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da hukumar FERMA.
Natasha Akpoti Uduaghan, wacce a da ke kula da kwamitin kula da harkokin cikin gida, yanzu ita ce ke jagorantar kwamitin da ke kula da ‘yan kasashen waje da kungiyoyin da ba na gwamnati ba.
Sauran nade-naden sun hada da “Sanata Garba Maidoki a matsayin shugaban kwamitin raya wasanni na majalisar dattawa da Joel Thomas a matsayin sabon shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin cikin gida, sai Victor Umeh wanda ya taba jagorantar kwamitin ‘yan kasashen waje, yanzu zai jagoranci kwamitin majalisar dattawa mai kula da hukumar yawan al’umma da NIMC”.
Majalisar dattijai ta kuma mika ta’aziyya ga kakakin majalisar bisa rasuwar tsohon mataimakin mai rinjaye na majalisar, Oriyomi Onanuga, a ranar 15 ga watan Janairu.
Akpabio ya jagoranci ‘yan majalisar wajen yin shiru na minti daya domin karrama shi kafin fara zaman majalisar.













































