DSS ta sake kama babban kwamandan kungiyar yan ta’adda ta Ansaru wanda ake zargi da jagorantar harin da aka kai wa Cocin Deeper Life Bible Church a Okene, jihar Kogi a ranar 7 August 2012 wanda ya jawo mutuwar mutum 19 ciki har da Fasto na cocin.
Rahotanni sun nuna cewa wadanda suka kai harin su uku ne dauke da bindiga ƙurar AK-47 kuma sun shiga cikin cocin suka bude wuta, lamarin da ya jawo raunuka ga mutane da dama da hallaka wasu masu ibada.
Bisa bayanan da hukumomin tsaro suka bayar, wanda ake zargin ya jagoranci harin ya kuma kaddamar da wani mummunan hari kan Bankuna biyar a Uromi, jihar Edo bayan harin cocin, inda aka hallaka jami’an tsaro da wasu mutane.
An kama shi tun farko amma ya tsere a lokacin harin da aka kai shi gidan yarin Kuje a watan Yulin 2022.
Majiyoyi sun bayyana cewa bayan an mayar da shi gidan yarin Kabba a watan Yunin 2022, ya amince cewa shi ne ya tsara yadda za a yi harin Kuje domin guduwa daga kurkuku.
A cewar majiyar, bayan fiye da shekaru uku da guduwarsa, jami’an DSS sun sake kama shi a safiyar ranar Juma’a ta hanyar wani shiri na sirrin leken asiri.
Kama shi ya zo ne kimanin wata biyu bayan hukumar ta gurfanar da wasu biyar da ake zargi da hannu a harin Cocin Catholic da ya faru a Owo, jihar Ondo a 2022.
A harin da aka kai Bankuna a Uromi a watan Fabrairu 2022, an hallaka jami’an ‘yan sanda da wasu kwastomomi, sannan an yi awon gaba da makudan kudade.
DSS na ci gaba da samun nasarori wajen kama ‘yan ta’adda da bata-gari a sassan kasar, tare da hanzarta gurfanar da wadanda aka kama.
Kazalika wanda ake zargin ya jagoranci wani hari da aka kai a ofishin yan sanda a yankin Auchi, wanda ya haddasa fargaba a cikin al’umma.









































