Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar kafa sabuwar Kwalejin Fasaha

WhatsApp Image 2025 11 14 at 18.22.46 750x430

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu kan dokar kafa sabuwar Kwalejin Fasaha a Gaya domin faɗaɗa damar ilimin gaba da sakandare a fadin jihar.

Wannan na cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar juma’a.

Jaridar SolaceBase ta rawaito cewa an gudanar da bikin sanya hannu a gidan Gwamnati tare da halartar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibril Ismail Falgore.

Haka kuma Mataimakin Kakakin Majalisar, Muhammad Bello Butubutu, ya halarta wajen gabatar da kudirin dokar tare da Kakakin Majalisar ga gwamnan domin amincewa.

Gwamnatin ta bayyana cewa kafa Kwalejin Fasaha a Gaya zai taimaka wajen horas da matasa a fannoni na fasaha da ƙwarewar da ake buƙata a kasuwanni.

A cewar sanarwar, wannan sabuwar kwalejin zata zama muhimmiyar hanya wajen bunƙasa ilimi da habaka ci gaban tattalin arzikin jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here