Kwastam ta ƙwato tabar wiwi ta kimanin naira miliyan 516 a Legas

323095337 4219191781538444 7225719497829188262 n
323095337 4219191781538444 7225719497829188262 n

Kontrolan hukumar ta kwastam a gaɓar tekun, Sani Yusuf, shi ya bayyana hakan a ranar Laraba a Legas yayin zantawa da manema labarai.

Yusuf ya ce an kwato tabar wiwi da ta kai kimanin naira miliyan 516 ne bayan samun bayanan sirri.

Ya kara da cewa an ɗauko tabar ne daga jirgin ruwa zuwa manyan motoci da nufin tafiya da su wani wuri kafin jami’ansa su dirar musu.

Ya kuma ce a ɗan tsakanin nan, tawagarsa ta kuma kwato jakukkuna 705 na shinkafar ƙasar waje mai nauyin kilo 50 wadda aka biya kuɗin shigo da shi kan naira miliyan 42 da kuma tarin tufafi.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, ya ruwaito kontrolan na cewa tsakanin watan Janairu zuwa Disamban 2022, sun samu nasarar ƙwato kayakin da aka haramta shigo da daban-daban waɗanda kuma kuɗinsu ya kai naira biliyan 9.

Ya gargadi masu shigo da kayakin da su daina abubuwan da suke yi, inda ya ce daga yanzu ba kaya kaɗai hukumar za ta ƙwato ba, har ma da kama ke take doka domin su fuskanci hukunci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here