Gwamnatin Jihar Kano ta kafa wani Kwamitin ba da Shawarwa mai mambobi 20 kan ilimi da kyautata rayuwar Almajirai, domin daidaitawa da kuma hade tsarin ilimin Tsangaya.
Musa Tanko Muhammad, Sakataren Yada Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG), ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Kano.
Ya bayyana cewa kwamitin yana karkashin jagorancin Babban Lauyan Jiha kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabir Maude.
Ya ce wannan yunkuri na da burin kyautata rayuwa da damar samun ilimi ga Almajirai tare da kiyaye tushen addini da al’adu na tsarin.
Haka kuma, ya bayyana cewa Amina Yusuf Yargaya, Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Kudi, ce za ta kasance Sakatariyar kwamitin.
Membobin kwamitin sun hada da wakilai daga gwamnati, masarautun gargajiya, kungiyoyin Musulunci, bangaren shari’a da ilimi da kuma kungiyoyin kare hakkin yara.
Ya bayyana cewa an ba kwamitin umarnin yin nazari kan yadda tsarin Tsangaya yake yanzu da kuma samar da tsari na ka’idoji, hadawa da kuma aiwatarwa.
Kwamitin zai kuma samar da taswirar aiwatar da aikin gwaji, sanya ido da dorewar sauye-sauyen da aka tsara.
A cewar sa, wannan sauyi na neman hada ilimin Alqur’ani da karatu, rubutu, lissafi, sana’o’i da kuma dabarun rayuwa, ba tare da barin tushen addini da al’ada na tsarin ba.
Ana sa ran kwamitin zai bada shawarwarin da za su hana cin zarafin yara, karfafa kare yara, da kuma tabbatar da dokar da za ta yi rajista, ba da lasisi da sa ido kan makarantun Tsangaya.
Haka zalika, kwamitin zai binciki hanyoyin samar da kudade masu dorewa tare da inganta alaka tsakanin malaman Alkur’ani, iyaye, malaman Musulunci, sarakunan gargajiya da al’umma.
Sakataren Gwamnatin Jiha, Umar Faruk Ibrahim, ya ce kwarewa da cancantan membobin kwamitin za ta taimaka wajen kyautata ilimi da jin dadin Almajirai.
Ya jaddada cewa ba a yi wannan sauyi ba don rushe ilimin Alqur’ani na gargajiya ba, sai don karfafa shi, kare yara daga cin zarafi da cin amana da kuma bai wa yaran dabarun da za su amfana da su a gaba. (NAN)












































