Ƴanbindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah na jihar Kwara

Gunmen scaled 1 750x430

Wasu ƴanbindiga ɗauke da makamai sun auka gidan shugaban ƙungiyar Miyatti Allah tare da halaka shi a ranar Asabar.

Kisan shugaban Miyetti Allah na jihar Kwaran na zuwa ne kusan wata biyu bayan kashe shugaban ƙungiyar na jihar Katsina, Alhaji Sirajo Ahmad Mairana.

Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun babban sakatarenta na ƙasa, Bello Aliyu Gotomo, ta yi Allah wadai da kisan da aka yi wa Idrissu Abubakar mai shekara 33.

Karanta: Yadda tsohon shugaban hukumar kula da shige da fice ya mutu a dakin otel, ba ‘yan bindiga suka kashe ba- ‘Yan sanda

Sanarwar ta ambato shugaban ƙungiyar na ƙasa, Baba Othman Ngelzarma na cewa an kashe Idrissu Abubakar da misalin ƙarfe 10:00 na dare bayan komawa gida daga sallar Tarawih.

Ƙungiyar ta ce cikin shekara biyu da suka gabata, ƴanbindiga sun kashe shugabanninta bakwai na jihohi da na ƙananan hukumomi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here