Hajj 2025: Kashim Shettima ya umurci NAHCON ta warware matsalolin da ka iya zama barazana

Kashim Shettima 750x430

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya tabbatar wa ‘yan Najeriya da ma al’ummar musulmi musamman cewa, babu wani mahajjaci dan Najeriya da zai rasa halartar aikin hajjin 2025.

Kashim Shattima ya umarci hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) da ta dauki dukkan matakan da suka dace don ganin an gudanar da aikin hajji cikin kwanciyar hankali ba tare da cikas ba ga dukkan maniyyatan kasar nan.

Wannan shi ne sakamakon ganawar da mataimakin shugaban kasar ya yi da shuwagabannin hukumar a ofishinsa da ke fadar shugaban kasa ta Villaa Abuja ranar Litinin.

Labari mai alaƙa: Babu wani Maniyyaci da zai rasa aikin Hajjin 2025 saboda soke kwangilar da aka yi – Shugaban NAHCON

Shettima ya kira taron ne biyo bayan rahotannin da ke cewa takaddamar kwantiragi da ma’aikatan Saudiyya, Mashariq Al-Dhahabiah, na iya haifar da hana alhazan Najeriya biza.

Ba za mu kyale duk wani mahajjaci dan Najeriya ya rasa aikin Hajjin 2025 ba. Aikin hajjin zai kasance babu kakkautawa, kuma kowane kalubale za a magance shi cikin gaggawa,” Shettima ya tabbatar a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha ya fitar.

Da yake maida jawabi game da batun soke kwangilar da aka yi da kamfanin da ke kasar Saudiyya, Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Saleh Usman, a safiyar yau ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa lamarin ba zai shafi aikin hajjin ba.

“Babu wani dalili na fargaba. Ba za a bar wani mahajjaci daya mai rijista a baya ba,” in ji Usman.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here