WOFAN ta karrama daliban da suka sauke Alkur’ani

WhatsApp Image 2026 04 27 at 08.07.17 750x430

Kungiyar Mata Manoma (WOFAN), ta karrama dalibai 32 da aka yaye daga makarantar Comprehensive Schools and Islamiyya a karshen mako, wadanda suka yi nasarar kammala karatun Alkur’ani mai girma kuma suka maimaita shi sau uku don tabbatar da dawwamammen karatu da ingantacciyar lafazi da fahimtar ainihin abin da Alkur’ani ya kaunsa.

SolaceBase ta ruwaito cewa an gudanar da bikin yaye daliban ne a harabar makarantar da ke Kano, wanda ya samu halartar manyan baki, malamai, iyaye, masana, da sauran jama’a daga ciki da wajen jihar.

Da take jawabi a wajen taron, mai makarantar kuma shugabar hukumar gudanarwa ta WOFAN, Dr Salamatu Garba, ta gode wa Allah madaukakin sarki bisa nasarar da ya baiwa daliban, ta kuma yaba wa iyayen daliban bisa kokarin da suka yi na tabbatar da cewa sun halarci azuzuwan karatu na yau da kullum da na musamman a wannan tafiya mai albarka.

Dr. Salamatu ta kuma yi kira ga iyaye da su ci gaba da ba da fifiko ga ilimi da tarbiyya ta gari ga ‘ya’yansu, inda tace dole ne kyawawan dabi’u da ladabi su kasance tare da kwarin gwiwa a karatu.

Haka zalika, ta kuma yaba wa bakin da suka halarci bikin bisa goyon baya da karfafa gwiwarsu da suke, yayin da ta bukaci daliban da ba su yi nasarar samun damar sauke Alkur ‘anin ba tare da wadannan rukunin da su ci gaba da jajircewa a karatunsu, don su shiga jerin wadanda za a yaye na gaba.
A wani bangare na bikin, makarantar ta gabatar da kyaututtuka da allunan sauka na musamman ga daliban da suka yaye.

Shugaban sashen Islamiyya, Malam Zakariyya Ahmed, ya ce daliban da suka yaye sun nuna kwarewa wajen karatun Alkur’ani kuma yanzu za su iya karanta Alkur’ani Mai Girma daga farko har karshe cikin gogewa. Ya bayyana cewa 19 daga cikin wadanda suka yaye mata ne, yayin da kuma sauran 13 maza ne.

Malam Ahmed ya yaba wa iyaye da masu kula da yara bisa jajircewarsu wajen tabbatar da zuwa makaranta akai-akai da shiga harkokin makaranta cikin himma. Ya kuma yaba wa malamai da shugabannin makaranta bisa jajircewa, hakuri, da kyakkyawan aiki wajen renon daliban zuwa ga kwarewa a karatun Alkur’ani.

Ya ba iyaye tabbacin cewa za a shirya karin azuzuwan karatu ga daliban da ba su kammala shirin ba, domin su samu matakin da ake bukata su shiga rukunin da za a yaye na gaba.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin masu ba da shawara, Farfesa Sani Miko, ya bayyana karuwar adadin wadanda suka yaye a wannan shekara a matsayin alama bayyananniya ta ci gaban makarantar.

A cewarsa, wannan nasara tana nuna irin tasirin da cibiyar ke yi, musamman ganin cewa yawancin wadanda suka yaye suna tsakanin shekaru 11 zuwa 15, yayin da wani dan shekara 9 ma ya fito a cikin wadanda suka yaye.

Ya bayyana cewa makarantar tana taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa iyaye wajen renon yara masu kyawawan dabi’u, yayin da ya yi kira ga iyalai da su ƙarfafa alakarsu da cibiyar ta hanyar tabbatar da zuwa a kan lokaci da halartar makaranta akai-akai.

Shima a nasa bangaren, babban limamin Darul Hadith, Dr Umar Ibrahim Indabawa, ya jaddada muhimmancin karatun Alkur’ani kuma ya bukaci wadanda aka yaye da su ci gaba da zurfafa fahimtarsu ta hanyar karanta ma’anoni da fassarar Alkur’ani Mai Girma.

Daya daga cikin iyayen daliban, Khadija Kabir, wadda ‘ya’yanta biyu suka kasance cikin wadanda suka yaye, ta nuna godiya ga Allah da shugabannin makaranta bisa jajircewarsu.

Ta yaba wa cibiyar bisa ingancin koyarwa, kulawa, da jajircewa wajen bunkasa dabi’a da ruhin yaran.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here