8Ministar harkokin jin kai da rage radadin talauci, Dr Betta Edu ta ce ana shirin yin kwaskwarimar shirin N-Power domin daukar karin mutane tare da tabbatar da biyan kudaden alawus-alawus din masu cin gajiyar shirin.
Edu ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a ranar Lahadin da ta gabata ta hannun mai ba ta shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Mista Rasheed Zubair, a Abuja.
Sanarwar ta ruwaito Ministan na cewa nan ba da jimawa ba za a magance kalubalen da masu cin gajiyar N-Power ke fuskanta ta fuskar jinkiri wajen biyan su alawus-alawus.
“Za mu canza hanyoyin ta yadda mutane za su dai na samu jinkirin wajan biyan su alawus dinsu.”
Ta kuma ce, ma’aikatar ta shirya kafa cibiyoyin bayar da agaji a fadin kananan hukumomi 774 na kasar nan, inda ta kara da cewa hakan zai kasance dogon buri na kawar da talauci a Najeriya.