Shugaban hukumar ‘yan sanda, Solomon Arase, ya ce jami’an soji da aka tura yankunan da ‘yan ta’adda ke gudanar da ayyukansu ba tare da wani horo ba, musamman a yankin Arewa maso Gabas, ba su da horo da sanin makamar tattara shaidu kan masu laifin, shi ya sa ake samun karuwar ayyukansu.
Arase tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sanda, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake sakin ‘yan fashin da aka kama su koma cikin al’umma ba tare da bayyana sunayensu ba, yana mai cewa a karshe akasarinsu sun koma aikata laifin, wanda hakan ke haifar da illa ga yankin.
Sai dai ya bukaci ‘yan sanda su karbe ragamar yaki da ta’addanci da sauran laifuffuka daga hannun sojoji, inda ya ce an horar da jami’an rundunar wajen tsare wuraren da ake aikata laifuka, da tattara shaidu da kuma gurfanar da masu laifi a gaban kuliya, wanda ya sha bamban da tsarin gudanar da aiki na rundunar soja.
An ruwaito Arase ya bayyana haka ne a Abuja lokacin da ya karbi bakuncin mai baiwa ‘yan sanda shawara, Lake Chad Basin Support Framework na hukumar kolin Burtaniya a Najeriya, Elizabeth Macleod; jagorancin ofishin sake fasalin ma’aikatan gwamnati karkashin jagorancin Darakta-Janar, D.I. Arabi da tawaga daga gidan TV na NTA da kuma News 24 karkashin jagorancin Janar Manaja, Fatima Abbas Hassan.













































