Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umarci duk masu rike da mukaman siyasa a gwamnatinsa da ke son tsayawa takara a zaɓen 2027 da su yi murabus kafin ko a ranar 31 ga Maris, 2026.
Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da ofishin sakataren gwamnatin tarayya ya fitar, wadda sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ya sanya hannu.
Takardar ta bayyana cewa wannan umarni ya yi daidai da sashe na 88(1) na dokar zaɓe ta shekarar 2026, da kuma jadawalin da Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar domin gudanar da zaɓukan fidda gwani gabanin babban zaɓen 2027.
Haka kuma takardar ta nuna cewa umarnin ya shafi dukkan nau’ikan masu mukaman siyasa na shugaban ƙasa da ke da niyyar shiga zaɓen fidda gwani ko neman tikitin takara.
Wadanda abin ya shafa sun haɗa da ministoci, kananan ministoci, masu ba shugaban ƙasa shawara na musamman, manyan mataimaka na musamman, mataimaka na musamman, mataimaka na kai tsaye, da kuma daraktoci-janar da shugabannin hukumomi, cibiyoyi da kamfanonin gwamnatin tarayya.
A cikin takardar da babban sakatare na sashen ayyuka na ofishin gwamnati, Ibrahim Kana, ya fitar, an bayyana cewa dole ne duk wadanda abin ya shafa su gabatar da takardun murabus dinsu ta ofishin sakataren gwamnatin tarayya kafin wa’adin da aka gindaya.
Shugaban ƙasar ya bayyana cewa wannan mataki ya zama dole domin tabbatar da bin dokokin zaɓe, inganta gaskiya da kuma samar da daidaito ga duk masu neman takara.
Ya kuma bukaci duk wadanda abin ya shafa da su bi wannan umarni yadda ya kamata, tare da tabbatar da kudurin gwamnatinsa na ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyya da kuma tabbatar da sahihancin tsarin zaɓe a ƙasar.













































