Gwamnan jihar Filato ya sauke mukarrabansa 6, ya dakatar da 1

GOV. Mutfwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya sallami mukarrabansa guda shida tare da dakatar da mutum guda.

Sakataren gwamnatin jihar, Samuel Jatau, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Jos.

Ya ce wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnati na sake fasalin ayyukanta domin inganta aiki da kuma samar da ingantacciyar hidima ga jama’a.

Daga cikin waɗanda abin ya shafa akwai Timothy Golu, mai bai wa gwamna shawara na musamman kan sadarwar dabaru, da Fom Gwottson, jami’in hulɗa na Jos ta Kudu, sai Nanbol Rimvyat da Nannim Langyi, jami’an hulɗa na Langtang ta Srewa.

Sauran sun haɗa da Paul Datugum da Nimchat Rims, jami’an hulɗa na Qua’an Pan da Langtang ta Kudu bi da bi.

Haka kuma gwamnan ya dakatar da Johnbull Shekarau, shugaban hukumar kula da ayyukan majalisar dokokin jihar, bisa halayen da suka saɓa da ka’idojin mukaminsa.

Sakataren gwamnatin ya umarci dukkan waɗanda abin ya shafa da su miƙa duk kadarorin gwamnati da ke hannunsu ga wuraren da suka dace.

Ya ƙara da cewa gwamnan ya gode musu bisa gudunmawar da suka bayar ga gwamnatinsa, tare da yi musu fatan alheri a rayuwarsu ta gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here