Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar mutane 18 sakamakon arangama tsakanin mambobin ƙungiyar masu sa kai da kuma ‘yan bindiga da suka tuba a ƙaramar hukumar Jibia.
Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin gida, Nasir Muazu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Katsina.
Ya ce rikicin ya faru ne a ƙauyukan Falale da Kadobe da ke ƙaramar hukumar Jibia a ranar 17 ga Maris.
Ya ƙara da cewa wasu mambobin ƙungiyar masu sa kai daga ƙauyukan da abin ya shafa sun yi arangama da ‘yan bindigar da suka tuba, lamarin da ya kai ga kashe wasu mutane uku daga cikinsu.
Hakan ya haifar da wani harin ramuwar gayya daga ‘yan bindiga, inda suka kai farmaki kan al’ummomin, wanda ya yi sanadin mutuwar ƙarin mutane 15.
Ya ce jami’an tsaro daga rundunar ‘yan sanda, jami’an tsaron farin kaya DSS, ƙungiyar sa kai ta Civilian Watch, da shugabannin al’umma sun haɗa kai domin shawo kan lamarin.
Ya bayyana cewa wannan haɗin gwiwa ya dakile ƙarin asarar rayuka tare da dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.
Ya bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu tare da bai wa jami’an tsaro damar kammala bincike.













































