Kano: Fashewar Bom ta hallaka mutane 5 tare da raunata wasu 10

Kano explosion 750x430

Mummunar fashewar wani abu ya faru a wani kamfani da ke Eastern Bypass a jihar Kano, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 5 tare da jikkata wasu 10.

Lamarin dai ya faru ne da safiyar yau Asabar, inda wani Bam da ake zargin ya na cikin wata babbar mota ya tarwatse.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano  Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

A cewarsa, motar da lamarin ya shafa ta fito ne daga jihar Yobe, ba tare da wani cikakken bayani ba.

Kwamishinan ƴan sandan ya ƙara da cewa har yanzu hukumomi ba su tabbatar da ainihin musabbabin fashewar ba, ko kuma mallakar abubuwan fashewar ba.

An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Aminu Kano AKTH, inda aka tabbatar da mutuwar mutane biyar, kuma 10 na samun kulawa.

Kwamishinan bai cewa tabbatar da ko akwai ma’aikata a cikin waɗanda abun ya shafa ba, yana mai cewa binciken zai bayyana wasu bayanai game da lamarin.

CP Bakori ya bayar da tabbacin cewa ƴan sanda za su gudanar da cikakken bincike don gano musabbabin fashewar.

Ya kuma buƙaci jama’a da su kwantar da hankulansu tare da bai wa hukumomi hadin kai domin gano musabbabin faruwar lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here