Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (FFS), shiyyar Jihar Kano, ta sanar cewa ta ceto mutum shida da ransu bayan da wani sashe na gini ya rufta a kamfanin sarrafa shinkafa na Whitefield Rice Mills Processing.
Kamfanin na nan a Karamar Hukumar Gezawa ta Jihar Kano.

Shugaban Hukumar a Jihar, Kazeem Sholadaye ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Al-Hassan Kanti ya fitar a ranar Talata a Kano.
Kanti ya ambato shugaban nasa yana cewa: “Mun sami kiran gaggawa daga wani Mista Johnson da misalin karfe 6:45 na yammacin ranar Litinin.

“Bayan samun rahoton, nan da nan muka tura jami’anmu na kashe gobara da masu aikin ceto daga Gidan Kashe Gobara na Danzaki.
“Kungiyar ceton ta yi amfani da shebura, injina da sauran kayan aiki don kwashe baraguzan ginin da kuma samun damar isa ga mutanen da suka makale.
“Sakamakon kwarewa da hadin gwiwar jami’anmu, an ceto mutane shida da rai daga ginin da ya rufta.”
Sholadaye ya kara da bayanin cewa babu wani da ya rasa ransa a lamarin, kuma rushewar ta faru ne saboda loda kayan amfanin gona da suka wuce kima a wani sashe na ma’ajiyar kamfanin.
Ya kara da cewa saboda hanzari da jami’an kashe gobarar suka yi, an ceto kadarorin da darajarsu ta kai kimanin naira miliyan 15, yayin da kadarorin da darajarsu ta kai naira miliyan 10 suka lalace.
Daga karshe, shugaban ya yi kira ga mazauna gari, masu gidaje, da masu ginin gidaje da su tabbatar da cewa gine-ginensu suna da kwari, su guji loda kaya masu nauyin da ya wuce kima, sannan gaggauta kai rahoton alamun lalacewar gini ga hukumomin da suka dace.
Sholadaye ya ce akwai bukatar gudanar da binciken gine-gine akai-akai da kuma bin ka’idojin kare lafiyar gine-gine domin hana rushewar gine-gine da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma











































