Gwamna Yusuf ya taya Gwamnatin Faransa murnar ranar kasar, ya nemi karin hadin gwiwa tsakanin Kano da Faransa

IMG 20260714 WA0345 750x430

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya gwamnati da al’ummar kasar Faransa murnar bikin zagayowar Ranar Kasar, inda ya sake jaddada kudurin jihar Kano na karfafa hadin gwiwa tsakaninsu da kasar Faransa a muhimman bangarorin ci gaba.

Hakan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Talata.

Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da aka gudanar a Ofishin Jakadancin Faransa da ke Abuja domin bikin.

Gwamnan ya jagoranci wata tawaga ta manyan jami’an gwamnati zuwa taron.

Ya taya Jakadan Faransa a Najeriya, Marc Fonbaustier, murna a madadin gwamnati da al’ummar jihar Kano, tare da yi wa kasar Faransa fatan dorewar zaman lafiya, arziki da ci gaba.

Gwamna Yusuf ya yaba da tsohuwar dangantakar da ke tsakanin Kano da Faransa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here