Tahirin Shugaban Amurka Donald Trump na fada da ‘yan jarida ba sabon abu ne, amma a wannan karon ba wai iya mummunar magana kawai ya yi ba, ya fice ana tsakiyar yin hira da shi. Inda ya kira ‘yar jaridar da “makaryaciya” kuma “mara gaskiya”.
A wata hira da Trump din ke yi da ‘yar jaridar NBC Kristen Welker a Wisconsin, inda ba tsammani ya fice daga tattaunawar bayan ta yi masa batun zargin da yayi a zaben gwamnan California.
“Ya ce kwanaki hudu da yin zabe, amma jami’an zabe ba su da niyyar sanar da sakamako ba.”
inda ya yi zargin cewa hakan ta Gary ne saboda ana yin magudi a zaben.
Trump ya kuma kafe cewa an yi magudi a zaben shugaban kasa na shekarar 2020 kuma “ana maimaita hakan yanzu haka a California.”
Da Kristen Welker ta nemi Trump ya kawo hujja kan zarge-zargen nasa, sai ya ce: “Ido ne kawai nawa.” Sannan sai ya tambaye ta: “Shin kina ganin ya dace su yi zabe, kwanaki biyar bayan haka ba su da shirin sanar da wanda ya yi nasara?”















































