Iran ta musanta cewa tana wata tattaunawa da Amurka a yanzu haka, bayan Shugaba Donald Trump ya ce za a fara sabbin tattaunawa a ranar Litinin domin kawo karshen yakin da ya shafe watanni shida ana yi.
Wannan raddin da Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi, ya biyo bayan jawabin Trump na cewa ya dage harin da zai kai wa Jamhuriyar Musuluncin domin ba da dama ga kokarin diflomasiyya, wani salo da aka saba gani a rikicin.
Washingon da Tehran sun shiga yaki ne tun a ranar 28 ga watan Fabrairu, lokacin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar da hare-haren bazata a kan Iran, ko da yake an samu lokutan kwanciyar hankali na wucin gadi sanadiyyar kokarin harkar diflomasiyya na tsawon watanni.
A makon da ya gabata, Trump ya yi barazanar kaddamar da gagarumin hari a kan Iran, inda rahotanni suka ce shugaban na Amurka yana duba yiwuwar kai sabbin hare-haren, inda ya kai hari kan kayayyakin makamashi.
Sai dai shugaban ya janye jiki daga wannan barazana a ranar Asabar, inda ya bayyana cewa an riga an tsara matakan yarjejeniyar.
Sai dai Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta musanta cewa ana tattaunawa a yanzu.
“Ba ma gudanar da wata tattaunawa da Amurka a yanzu. Tattaunawar mu na gudana ne da Oman domin tabbatar da hanyar wucewa ta Mashigar Hormuz,” in ji Kakakin Ma’aikatar, Esmaeil Baqaei, a yayin wata ganawa da manema labarai.
Mashigar Hormuz batu ne mai matukar rikitarwa a kokarin kawo karshen yakin. Iran na hana jiragen ruwa wucewa ta wannan muhimmin hanyar kasuwanci, har ma tana harba wa jiragen kasuwanci makamai.
Kafin barkewar yakin, ana wucewa batare da wata matsala ba ta wannan Mashiga, amma yanzu Iran na son rike iko da ita da kuma karban kudi, abin da Amurka ta ki amincewa da shi.
Tehran ta ki barin jiragen su bi wata hanya face wadda ke bin gabar tekun Iran.
A ranar Lahadi, Baqaei ya shaida wa gidan talabijin na gwamnati cewa an kusa cimma yarjejeniya kan yadda za a tafiyar da Mashigar Hormuz tare da kasar Oman, wadda ke gefen kunkuntar hanyar ruwan.
“Mun kusa cimma matsaya kan hanya da zata dace da bangarorin biyu – ba arewa ko kudunci ba, amma wadda ke mutunta hakkokin ikon mallakar bangarorin biyu tare da kare muradun mu na kasa da tsaron mu,” in ji shi.
















































