Ofishin Jakadancin Amurka ya gargadi ‘yan Najeriya kan amfani da hotunan fasfo da aka gyara da AI

US Mission 750x401

Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya gargadi masu nema fasfo da su guji amfani da hotunan da aka gyara da Kirkirarriyar Basira (AI) ko da na’ura, yana mai cewa ba za a amince da irin wadannan hotuna ba.

A cikin wani sakon tunatarwa da ofishin ya wallafa a shafin X a ranar Juma’a, ya jaddada cewa hotunan fasfo dole ne su kasance na gaskiya, na kwanan nan kuma su nuna yadda mai nema yake a yanzu.

Ofishin Jakadancin ya ce masu nema su guji amfani da kayan aikin AI, hotunan da aka gyara ko duk wani irin gyaran na’ura yayin daukar hoton fasfo.

“Tunatarwa! KADA ku yi amfani da AI ko kayan gyaran hotun na’ura a hoton fasfon ku. Ba za mu amince da hotunan da aka gyara ko aka tace ba,” in ji ofishin.

Ya kara da cewa dole ne a dauki hoton fasfo cikin watanni shida da suka gabata, kuma ya kamata ya yi kama da mai nema don jami’an iyakar Amurka TSA ko CBP su iya gane shi cikin sauki.

“Hotonku ya kamata ya kasance na kwanan nan, a dauke shi cikin watanni shida da suka gabata kuma ya yi kama da ku jami’in TSA ko CBP dole ne ya iya gane cewa ku ne,” in ji sanarwar.

Ofishin ya kuma gargadi cewa mika hoton da aka gyara da na’ura zai iya jinkirta aikin sarrafa neman fasfo sosai.

“Mika hoton da aka gyara da na’ura zai jinkirta neman ku sosai.”

An kuma umurci masu nema da su koma shafin jagororin hoton fasfo na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka don karin bayani kan ka’idojin da ake bukata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here