
Dubun dubatar mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a Washington da sauran manyan biranen Amurka a jiya Asabar inda suke tur da Shugaba Trump da kuma abin da suka kira manufofinsa na kama-karya.
Ita ce zanga-zanga mafi girma da aka yi a yini guda don nuna adawa da ƙudirorin Trump tun bayan komawarsa Fadar White House.
Masu zanga-zangar sun yi Allah wadai da yadda aka kori ma’aikatan gwamnati daga aiki da sabbin harajin kasuwanci da ya ƙaƙaba wa ƙasashe.
A cewar wakilin BBC wasu sun soki manufofinsa na ƙasashen waje, wasu sun ɗaga tutar Ukraine yayin da wasu kuma suka riƙe tutar nuna goyon baya ga Falasɗinawa.
Galibin mutanen sun ce matakan da gwamnatin Tump ke ɗauka za su yi wa tattalin arziki illa tare da raunata Amurka.