Yan sanda sun yi gargadi kan zanga-zangar da za a yi a fadin kasa baki daya

IGP kayode egbetokun

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi gargadi kan gudanar da zanga-zangar da wata kungiya mai suna ‘Take It Back Movement’ za ta gudanar a ranar Litinin 7 ga Afrilun 2025 a fadin Jihohin kasar nan, musamman ma birnin tarayya Abuja.

Rundunar‘yan sandan, ta ce ranar 7 ga watan Afrilu, rana ce da gwamnatin tarayya ta ware a matsayin ranar ‘yan sanda ta kasa domin murnar jajircewa da sadaukar da kai da jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya suka yi, inda ta ce zabar ranar da za a gudanar da zanga-zangar da kungiyar ta yi na dauke da wani manufa ta daban.

Wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar (FPRO), ACP Olumuyiwa Adejobi, a ranar Lahadi, ta ce rundunar yan sanda ba ta adawa da amfani da ‘yancin ‘yan kasa na gudanar da taro da zaman lafiya a Nijeriya kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada.

A cewar sa, sai dai ta damu matuka da dalilin da ya sa aka shirya irin wannan zanga-zangar da aka a wannan rana da ake tunawa da irin gudunmawar da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta bayar wajen samar da tsaro a kasa baki daya.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya karkashin jagorancin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, Ph.D., NPM, yayin da yake jaddada aniyar hukumar ta NPF na gudanar da aikinta yadda ya kamata kamar yadda doka ta tanada da kuma mutunta ‘yancin ‘yan kasa, ya bukaci duk wadanda suka shirya zanga-zangar da kuma daidaikun mutanen da suke da niyyar shiga zanga-zangar da su janye aniyar su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here