Hukumomin ƙasar Saudiyya sun amince da ɗaukar gawar marigayi dattijo kuma hamshakin ɗan kasuwa Alhaji Aminu Alhassan Dantata daga Abu Dhabi zuwa birnin Madina domin binne shi.
Babban sakataren marigayi Dantata, Alhaji Mustapha Abdullahi Junaidu, ne ya sanar da hakan a yau Lahadi a shafinsa na Facebook.
“An tabbatar da cewa Aminu Alhassan Dantata za a dauke shi daga Abu Dhabi zuwa birnin Madina domin gudanar da jana’izarsa, hukumomi sun ba da izinin kai shi can, kuma ana shirye-shiryen gudanar da sallar jana’izarsa gobe da safe In sha Allah.” Inji Junaidu.
Ya bayyana cewa, jinkirin da aka samu na kammala shirye-shiryen binnewar ya biyo bayan karshen mako ne, wanda ya shafi yadda ake tafiyar da bayanan da suka dace da kuma amincewa.
A baya dai SolaceBase ta ruwaito cewa Alhaji Aminu Dantata shahararren attajiri kuma mai taimakon jama’a, dan kasuwa kuma dattijon ƙasa, ya rasu da tsakar daren wayewar ranar Asabar.













































