Har yanzu Akume ne Sakataren gwamnatin tarayya- Fadar shugaban ƙasa

George Akume SGF 750x430

Fadar shugaban ƙasa ta musanta naɗin sabon sakataren gwamnatin tarayya, inda ta ce Sanata George Akume ne ke ci gaba da zama a matsayinsa na sakataren gwamnatin tarayya.

Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar da tsakar daren wayewar yau Lahadi.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa hakan ya biyo bayan wani labari da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani, wanda ke nuni da cewa an nada Hadiza Bala Usman a matsayin sabuwar Sakatariyar gwamnatin tarayya.

Sanarwar ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ke Saint Lucia a halin yanzu bai naɗa wani sabon muƙami ba.

”Bayanin da ke yawo game da maye gurbin Akume ba gaskiya ba ne. Wasu masu yaɗa ƙarya ne suka kirkiro shi, in ji sanarwar.

Fadar shugaban ƙasa ta shawarci ‘yan Najeriya da su riƙa yin watsi da labaran karya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here