Shugabannin Afirka sun tafi taron Amurka da Afirka a Washington

FB IMG 16708398025919703
FB IMG 16708398025919703

Shugabannin Afirka sun tafi Washington gabanin taron Amurka da kasashen Afirka da shugaba Biden zai dauki nauyi.

Taron na yini uku za a fara ne daga ranar Talata, kuma zai mayar da hankali ne a kan kokarin da gwamnatin Biden ke yi ga kasashen Afirka.

Shugabanni kasashen Afrika 49 da kuma shugaban hukumar tarayyar Afirka Moussa Faki Mhamat ne aka gayyata taron.

Ba a gayyaci shugabannin kasashen Mali da Sudan da kuma Burkina Faso ba, saboda dakatar da su da kungiyar tarayyar Afirka ta yi, Eritrea ma ba za ta halarci taron ba.

Tuni wasu daga cikin shugabannin da suka tafi taron suka wallafa batun tafiyar tasu a shafukansu na tiwita.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here