Kungiyar Renewed Hope Youth Engagement (RHYE) ta kaddamar masu gudanarwarta reshen Jihar Kanao tare da sauran masu gudanarwa na yankuna na Kano ta Tsakiya, ta Arewa da kuma ta Kudu a matsayin wani bangare na kokarin karfafa tattara jama’a daga matakin kasa da fadada shigar matasa cikin mulki da siyasa.
Sabon mai gudanarwa na (RHYE) na Jihar Kano, Dr Dahir M. Hashim wanda kuma kwamishinan ruwa da muhalli ne na Jihar Kano, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Juma’a.
Ya ce kaddamarwar ta kafa ginshiki na tsari da dogaro da fasaha wanda aka kebe domin tattara matasa, fito da nasarorin gwamnati, karfafa hadin gwiwa da al’umma da karfafa siyasa mai ma’ana.

Dr. Hashim ya yi godiya bisa amincewar da aka nuna masa na jagorantar kungiyar a Jihar Kano, yana mai cewa nadin damar ba da gudummawa ga karfafa matasa da ci gaban siyasa ne.
“Na ji dadin amincewar da aka nuna min na jagorantar wannan muhimmiyar tafiya a Jihar Kano,” in ji shi.
A cewarsa, taron ya samu halartar shugaban RHYE na kasa, Abdulaziz Abubakar Kaka, kwamishinan lantarki na Jihar Kano, Dr. Gaddafi Sani Shehu, Kwamishinar Muhalli ta Jihar Kwara, Hajiya Nafisat Musa Buge, da masu gudanarwa na jihohin Filato, Kaduna da Yobe sun halarci bikin kaddamarwar.











































