Hukumar Shiryawa da Kula da Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandare ta Kasa (JAMB) da Hukumar Jarrabawar Afirka Ta Yamma (WAEC) sun fayyace cewa daliban da ke neman gurbi a manyan makarantu za su biya kudi naira 4,000 sau daya kacal domin tantance sakamakon jarrabawar su ta O’Level.
Hukumomin jarrabawar guda biyu sun yi wannan karin hasken ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a ranar Talata a Abuja, biyo bayan shawarwarin da aka yi kan sabuwar manufar da aka fito da ita na tantance sakamakon jarrabawar manyan makarantun sakandare na Afirka ta Yamma (WASSCE/O’Level).
Sun bayyana cewa daliban da JAMB ke da hakkin daidaitawa da kula da shigar su makaranta za su tantance sakamakon su na WAEC sau daya ta hanyar JAMB.
Sun kara da cewa, daga baya za a tura sakamakon tantancewar zuwa ga babbar makarantar da dalibin ke neman gurbi a cikinta.
Bisa ga bayanin sanarwar, ana bukatar dalibai su biya kudi naira 4,000 kacal don wannan aikin na tantancewa ta hanyar tsarin JAMB na musamman da aka ware, ba wai ta hanyar makarantun da suke son shiga ba.
Hukumomin sun ce manyan makarantun za su yi amfani da sakamakon da JAMB ta tantance kuma ta raba musu domin tantance dalibai, tsara shigar da dalibai da sauran ayyukan gudanarwa.
“Ba za a bukaci dalibai su sake biyan kudi don wani tantancewa daban ba.”
Haka kuma sun bayyana cewa WAEC ta ba JAMB izinin raba sakamakon tantancewar da manyan makarantun da abin ya shafa domin manufofin da aka ambata.
Sun bayyana cewa an tsara wannan tsari ne domin tabbatar da cewa ɗaliban da suka yi nasarar tantance sakamakon su na WASSCE O’Level ba za su sake fuskantar bukatar maimaita tsarin ba.
A cewarsu, wannan yanke shawara zai rage wahala da kuma tsadar kudaden da ke tattare da yawan zirga-zirga zuwa manyan makarantu ko kuma cibiyoyin jarrabawa ta kwamfuta (CBT) da JAMB ta amince da su.
Hukumomin sun ce dalibai za su iya fara tsarin tantancewar daga kwanciyar hankali a gidajensu ko kuma kowane wuri da ke da hadin yanar gizo.
Saboda haka, sun karfafa gwiwar dalibai da su amfana da wannan tsari ta hanyar tantance sakamakon jarrabawar su ta WASSCE O’Level ta hanyar aikin tantancewa na JAMB sau daya kacal, tare da lura cewa makarantar da abin ya shafa za ta yi amfani da sakamakon da aka tantancewar.
Sun bayyana cewa wannan hadin gwiwa tana nuna sadaukarwar su wajen sanya bukatun dalibai a gaba, rage kudaden da ba su da mahimmanci da kuma saukake tsarin shiga makarantu tare da kiyaye daraja da tsaron bayanan karatun dalibai. (NAN)












































