Gwamnatin Tarayya ta shawarci ’yan Najeriya, musamman masu fama da wasu cututtuka, da su yi taka-tsantsan yayin da suke bi ta birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha, biyo bayan mutuwar ’yan Najeriya 16 a birnin a cikin shekarar nan.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ce ta fitar da wannan sanarwa a ranar Juma’a, inda ta bayyana cewa ofishin jakadancin Najeriya da ke Addis Ababa ya samu rahoton mutuwar ’yan Najeriya 16 da ke bi ta birnin, waɗanda ake zargin matsalolin lafiya da ke da alaƙa da tsayin birnin sama da matakin teku ne suka haddasa mutuwarsu.
Read also: Saudiyya ta saki ‘yan Najeriya 3 da aka cafke bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi
A cewar ma’aikatar, birnin Addis Ababa yana da tsayin kusan mita 2,355 sama da matakin teku, lamarin da ke haifar da raguwar matsin iskar sararin samaniya da kuma ƙarancin iskar Oxygen da ake samu.
Ma’aikatar ta bayyana cewa duk da cewa mafi yawan mutane masu ƙoshin lafiya na iya sabawa da irin wannan yanayi, masu fama da cututtukan zuciya da na numfashi na iya fuskantar haɗarin matsalolin lafiya.
“A cikin shekarar nan, ofishin jakadancin Najeriya da ke Addis Ababa ya samu rahoton mutuwar ’yan Najeriya 16 da ke bi ta birnin, waɗanda ake zargin matsalolin lafiya da ke da alaƙa da tsayin birnin ta sama da matakin teku ne suka haddasa mutuwarsu.”
Read also: Tawagar ƙwararru ta NAHCON ta tashi zuwa Makkah domin kaddamar da aikin Hajji
Saboda haka, gwamnatin ta buƙaci ’yan Najeriya masu fama da cututtukan da ka iya tsananta sakamakon kasancewa a wuraren da suke da tsayi sosai sama da matakin teku, da su nemi shawarar likitoci kafin yin balaguro ta Addis Ababa.
Ma’aikatar ta ƙara da cewa “an shawarci matafiya masu fama da wasu cututtuka da su nemi shawarwarin likitoci da suka dace kafin gudanar da irin waɗannan tafiye-tafiye.”
Sai dai gwamnatin tarayyar ta jaddada cewa wannan gargadi ba yana nufin tana hana ’yan Najeriya zuwa Addis Ababa ko bi ta birnin ba ne.
“Maimakon haka, manufar ita ce tabbatar da cewa mutanen da matsalolin lafiyarsu ka iya shafar sakamakon ƙarancin iskar Oxygen a wurare masu tsayi sun samu cikakken bayani tare da ƙarfafa musu gwiwar ɗaukar matakan kariya da suka dace.”
Read also: DSS ta gurfanar da Emefile a gaban kotu
A ƙarshe, ma’aikatar ta sake jaddada aniyar gwamnatin na kare lafiya, tsaro da jin daɗin ’yan Najeriya da ke ƙasashen waje, ta hanyar fitar da shawarwarin tafiye-tafiye a kan lokaci da kuma samar da sauran tallafin ofishin jakadanci.












































