Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya fice daga jam’iyyar APC a hukumance inda ya koma jam’iyyar Social Democratic Party (SDP).
A wata takardar murabus da El-Rufai ya aike wa gundumarsa a ranar Litinin, ya bayyana rashin jituwa da shugabannin jam’iyyar tare da nuna rashin jin dadinsa kan alkiblar da jam’iyyar ta ke kai a yanzu a matsayin abinda ya sanya shi ficewa daga cikin ta.
“Na yi wa jam’iyyar APC hidima da himma kuma na bayar da gudunmawa sosai wajen ganin ta samu nasarar zama dandalin siyasa,” in ji shi.
Karin karatu: El-Rufai ya gana da Aregbesola, Tunde Bakare gabanin zaben 2027
“Duk da haka, abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun nuna rashin mutunta ka’idojin dimokiradiyya da ci gaban dabi’un da nake da su.”
A matsayinsa na wanda ya kafa jam’iyyar APC, El-Rufai ya taka rawar gani a zabukan 2015, 2019, da 2023.
Da yake yin tsokaci kan zamansa na gwamna, ya bayyana yadda gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen bunkasa dan Adam, ilimi, kiwon lafiya, samar da ababen more rayuwa, samar da ayyukan yi, da zuba jari.
Ya bayyana cewa, akwai damuwa da ta fuskar tafiyar da harkokin mulki da tafiyar da jam’iyyar a cikin gida.
Da ya koma SDP, El-Rufai ya bayyana godiyarsa ga mashawartansa, abokan aikinsa, da magoya bayansa, inda ya jaddada kudirinsa na bin tsarin dimokuradiyya.
“A matsayina na dan jam’iyyar SDP, na kuduri aniyar samar da hadin kan dimokradiyya domin kalubalantar jam’iyyar APC a zabe mai zuwa,”.