Fitaccen malamin addinin Musulunci na Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi, ya mayar da martani kan rasuwar Jagoran Koli na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, inda ya bayyana shi a matsayin “mai sa’a.”
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, Gumi ya ce Khamenei ya rasu ne a abin da ya kira jihadi kan waɗanda ke kashe mata da yara marasa laifi a Gaza da sauran wuraren da ake fama da rikici.
Ya ce jinin marigayin zai zama abin da zai haifar da sauyi a cikin al’ummar Musulmi, yana mai cewa Khamenei ya tsaya tsayin daka kan adalci kuma bai ɓuya ba.
Gumi ya kuma yi gargaɗi ga waɗanda ya zarga da hannu a rasuwar Khamenei, yana cewa lokaci zai nuna irin sakamakon da za su fuskanta a duniya.
Maganganun nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun martani daga ƙasashen duniya bayan rahotannin rasuwar Khamenei, lamarin da ya haifar da muhawara a fannoni na siyasa da addini.













































